ABNA24 : A cikin sakonsa na taya murna, shugaban kasar ta Iran, ya yi fatan, fadada alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma inganta dangantaka stakanin Teheran da Dakar, a fannoni da dama.
Dakta Rohani, ya kuma yi wa Senegal, fatan wadata, ya kuma ce kasashen biyu zasu iya cin amfanin alakar dake tsakaninsu ta fuskar kimiya, al’adu, fasaha da kuma jami’o’i.
A rana irin ta yau 4 ga watan Afrilu ne Kasar Senegal dake yankin yammacin Afrika, ta samu yancin kanta daga turawa ‘yan mulkn mallaka na kasar Faransa.
342/